logo

HAUSA

Wani harin BH ya yi sanadin mutuwar fararen hula 2 a Kamaru

2022-02-16 11:41:19 CRI

Wani harin BH ya yi sanadin mutuwar fararen hula 2 a Kamaru_fororder_0216-Boko Haram-Fa'iza

A kalla fararen hula 2 ne suka mutu, biyo bayan wani harin da mayakan BH suka kai wani kauyen dake yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru, ranar Litinin da daddare.

Wani jami’in tsaro da ya bukaci a boye sunansa, ya shaidawa Xinhua cewa, mayakan sun kai harin ne kauyen Gaboua na yankin Koza, yayin da mazauna ke bacci. Inda suka shiga gidan wani fitaccen mutum, suka kuma kashe shi tare da dansa.

Har ila yau, mazauna kauyen sun ce wani gungun ’yan ta’addan kuma, sun shiga sun yi sata a gidaje da dama a kauyen Biguide dake yankin, sai dai babu asarar rai a nan.

Cikin makwannin baya-bayan nan, mayakan na BH, suna kara kai hare-hare kan fararen hula a yankin, inda suke farwa yankuna masu rauni dake fama da talauci. (Fa’iza Mustapha)