logo

HAUSA

An Yi Murnar Bikin Kunna Fitilu Na Yuanxiao A Sassa Daban Daban na kasar Sin

2022-02-16 13:47:52 CRI

An Yi Murnar Bikin Kunna Fitilu Na Yuanxiao A Sassa Daban Daban na kasar Sin_fororder_biki

A karshen lokacin hutu na murnar Bikin Bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, an yi murnar bikin kunna fitilu na Yuanxiao a sassa daban daban na kasar, inda aka ji dadin kallon fitilu masu siffofi daban daban, da gasar kacici kacici da dandana abincin Yuanxiao, a kokarin bayyana kyakkyawan fatan mutane kan zaman rayuwa mai dadi.

A bikin nune-nunen fitilu a wurin shan iska na gwada lambuna na Zhengzhou dake lardin Henan, fasahar zamani ta haskaka wata al’adar gargajiyar Sinawa wato kallon fitilu. Fitilu masu siffofi daban daban wadanda aka kera bisa fasahohin zamani sun haskaka duhun dare, sun kuma sanya bikin kunna fitilu na Yuanxiao ya amsa sunansa sosai.

Ban da haka kuma, a jajibirin bikin na Yuanxiao, an yi gasar kacici kacici domin murnar bikin a birnin Tongling na lardin Anhui, inda mutane masu tarin yawa suka halarta. Ke Zi’ang, wani mazauni birnin ya ce, “Gasar kacici kacici a bikin Yuanxiao ya taimaka min kara fahimtar basirar al’ummar Sinawa da ma al’adunmu mai dogon tarihi. A gani na, murnar wannan biki ta hanyar gargajiya yana da matukar ban sha’awa.” (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan