logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su ci gaba da taimakawa Somaliya yadda ya kamata

2022-02-16 11:44:35 CRI

Sin ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su ci gaba da taimakawa Somaliya yadda ya kamata_fororder_hoto1

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa, su ci gaba da taimakawa kasar Somaliya kamar yadda take bukata.

Dai Bing ya bayyana haka ne jiya, lokacin da yake jawabi ga taron tattauna batun kasar Somaliya, da aka yi a kwamitin sulhu na MDD.

A cewarsa, a ’yan kwanakin baya-bayan nan, kasar Somaliya ta cimma nasarar ciyar da yunkurin zabe gaba. Don haka, ya kamata gamayyar kasa da kasa su tsaya tsayin daka kan ka’idar “jagorancin jama’ar kasar Somaliya, da ’yancin kansu”, da kuma goyon bayan kasar wajen neman farfadowa, da taimaka mata kamar yadda take bukata, a maimakon matsa mata lamba.

Haka kuma, ya kara da cewa, Somaliya kasa ce mai muhimmanci a kahon nahiyar Afirka, don haka, zaman lafiyar kasar na da muhimmanci wajen kare yanayin tsaron yankin baki daya.

Har ila yau, ya ce kasar Sin ta fidda shawarar “Neman ci gaban kahon Afirka cikin zaman lumana” domin taimakawa kasashen yankin fuskantar kalubale a fannonin tabbatar da tsaro da neman ci gaba, da kuma gudanar da harkokin kasashensu.

Bugu da kari, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan kasashen yankin wajen neman hanyoyin ci gaba bisa yanayin da suke ciki. Kana, tana goyon bayan kahon Afirka wajen shimfida yanayin hadin gwiwa, zaman karko, da zaman lumana, ta hanyar warware matsalolin dake shafar kabilu, da addinai da kuma yankin iyaka tsakanin kasa da kasa, ta hanyoyin da suka dace. (Maryam)