logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya bukaci a yi amfani da hikima wajen inganta ayyukan gwamnati

2022-02-16 11:15:17 CRI

Firaministan kasar Sin ya bukaci a yi amfani da hikima wajen inganta ayyukan gwamnati_fororder_0216-Chinese premier-Fa'iza

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi kira da a tattaro hikimomi ta kowane bangare, domin inganta ayyukan gwamnati, da daukar matakan da suka dace na bunkasa tattalin arzikin masana’antun kasar da bangaren samar da hidimomi.

Yayin da yake jagorantar taron majalisar zartarwar kasar, Li Keqiang ya yi bayani kan yadda za a tafiyar da shawarwarin da mambobin majalisar wakilan jama’a NPC da mambobin kwamitin tuntuba kan harkokin siyasa na CPPCC suka gabatar a shekarar 2021.

A bara, ofisoshi da sassan dake karkashin majalisar zartaswar, sun nazarci shawarwari 8,666 da wakilan majalsar wakilan jama’a na NPC suka gabatar, wanda shi ne kaso 96.4 na jimilar shawarwarin da aka samu a shekarar, kana sun nazarci wasu kudurori 5,718 da mambobin kwamitin CPPCC suka gabatar, wanda shi ne ya dauki kaso 93.4 na jimilar kudurorin da aka gabatar a shekarar.

Taron ya bayyana cewa, hukumomi masu ruwa da tsaki sun amince da shawarwari sama da 4,300 inda daga bisani suka aiwatar da matakai sama da 1,600.

A cewar taron, bangaren masana’antu da samar da hidimomi, sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da dorewar habakar tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

Bisa la’akari da cewa tattalin arzikin bangaren masana’atu bai kammala farfadowa ba, haka kuma wasu bangarorin bada hidima na fuskantar kalubale saboda COVID-19, kasar za ta kaddamar da wasu matakai domin kara karfafa bangarorin.

Daga cikin matakan akwai inganta sokewa da rage haraji a bangarorin masana’antu da na bada hidima, da fadada rage haraji da sauran kudaden da ake biya da kuma tsawaita lokacin biyan haraji ga kanana da matsakaitan masana’antu. (Fa’iza Mustapha)