logo

HAUSA

Adadin masu kallon gasar Olympics ta Beijing a kafar talabijin ya karya matsayin bajimta

2022-02-16 19:36:08 CRI

Adadin masu kallon gasar Olympics ta Beijing a kafar talabijin ya karya matsayin bajimta_fororder_olympic

Babban jami’in sashen kasuwanci a bangaren kafar talabijin, karkashin kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa, Timo Lum, ya ce adadin masu kallon gasar Olympics ta birnin Beijing ta kafar talabijin ya karya matsayin bajimta, inda ya zuwa Larabar nan, adadin ya haura na ragowar gasannin Olympics da aka gudanar a baya.

Timo Lum, wanda ya bayyana hakan, yayin taron da cibiyar yada labarai ta gasar dake nan birnin Beijing ta shirya a karo na 12 tun bayan bude ta, ya jinjinawa nasarar da kafar CMG ta cimma, a fannin jagorantar nuna shirye shiryen gasar ta lokacin hunturu ta shekarar 2022 cikin nasara, inda shirye shiryen suka yi matukar kayatar da al’ummun kasa da kasa.  (Saminu)