logo

HAUSA

Shugaba Xi ya zanta da takwaransa na kasar Faransa

2022-02-16 19:58:48 CRI

Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron ta wayar tarho. Yayin zantawar ta su, Xi Jinping ya jaddada cewa, a wannan sabuwar shekara, Sin da Faransa za su ci gaba da cudanya bisa ginshikin martaba juna da adalci. Kaza lika za su karfafa tattaunawa, da musaya a matakai daban daban, tare da bunkasa fahimta da amincewa juna.

A nasa bangare kuwa, shugaba Macron cewa ya yi, halin da ake ciki yanzu haka, game da batutuwan kasa da kasa na cike da matsi da hargitsi. Don haka Faransa ke fatan zurfafa cikakken hadin gwiwa tsakanin ta da kasar Sin.  (Saminu)