logo

HAUSA

An cimma gagarumar nasara a gina tsarin inganta muhallin halittu a birnin Beijing

2022-02-15 20:16:27 CRI

An cimma gagarumar nasara a gina tsarin inganta muhallin halittu a birnin Beijing_fororder_muhalli

Cibiyar watsa labarai ta birnin Beijing, ta shirya taron manema labarai na musamman, game da gina tsarin inganta muhallin halittu a birnin, inda a yayin taron na yau Talata, mataimakin darakta, kuma kakakin hukumar kare muhallin halittu da sauran sassan muhalli na birnin Yu Jianhua, ya ce a shekarar 2021 da ta gabata, adadin kwanakin da aka samu tsaftacacciyar iska a birnin Beijing, ya karu zuwa kwanaki 288, adadin da ya kai kaso 78.9 bisa dari na jimillar kwanakin shekarar.

Yu Jianhua ya kara da cewa, birnin Beijing yana nacewa manufar samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu bisa yanayin kare muhalli.  (Saminu)