logo

HAUSA

Dan wasan kasar Sin Su Yiming ya samo mata lambar Zinare na 6 a wasannin Olympics na hunturu dake gudana

2022-02-15 15:45:49 CRI

Dan wasan kasar Sin Su Yiming ya samo mata lambar Zinare na 6 a wasannin Olympics na hunturu dake gudana_fororder_220215-faeza-Olympics gold

Dan wasan kasar Sin Su Yiming ya lashe lambar zinari a wasan zamiyar kankara ta Snowboard ajin maza, da maki 182.50, wanda ya kawo lambobin yabo na zinare da Sin ta samu zuwa 6.

Dan wasan kasar Sin Su Yiming ya samo mata lambar Zinare na 6 a wasannin Olympics na hunturu dake gudana_fororder_220215-faeza-Olympics gold2

Baya ga haka, Gu Ailing Eileen ta kasar Sin ta lashe lambar azurfa a zamiyar kankara ta Slopestyle, wannan ita ce lambar yabo ta biyu da ’yar wasan ta samu a wasannin Olympics na lokacin hunturu dake gudana.

Kasar Sin na da lambobin yabo 12 da suka hada da zinare 6 da azurfa 4 da kuma tagulla 2, inda ta kafa sabon tarihi a wasannin Olympics na lokacin hunturu.  (Fa’iza Mustapha)