logo

HAUSA

Beijing 2022: Yawan ’Yan Wasa Mata Sun Kafa Tarihi

2022-02-15 14:33:31 CRI

Beijing 2022: Yawan ’Yan Wasa Mata Sun Kafa Tarihi_fororder_mata

Tashar yanar gizo ta jaridar Neues Deutschland ta kasar Jamus, ta ruwaito a kwanan baya cewa, an kafa tarihi a yawan ’yan wasa mata da suka shiga gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta shekarar 2022. A cikin dukkan ’yan wasa kimanin 2900, kaso 45 cikin dari mata ne. Sakamakon gasar da ke gudana yanzu, ya sa ana kara samun daidaito a tsakanin mata da maza a gasar wasannin Olympics.

A yayin gasar da aka yi a Tokyo na kasar Japan, ’yan wasa mata na kasar Sin sun fi maza na kasar yawa da fiye da ninki biyu, yayin da gasar da ke gudana a Beijing, aka samu ’yan wasa mata 87 da maza 89 cikin kungiyar ’yan wasan kasar Sin.

Kamfanin dillancin labaru na Agence France-Presse (AFP) ya labarta cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, ta fi samun daidaiton adadi tsakanin maza da mata a tarihi. A ganin ’yan wasa, kara yin takara tsakanin kungiya mai hadakar mata da maza na da ma’ana sosai, lamarin da ya taimaka wajen kyautata matsayin wasannin mata. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan