logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a mayar da hankali kan muhimman bangarori 4 da suka shafi yaki da talauci

2022-02-15 11:32:35 CRI

Kasar Sin ta yi kira da a mayar da hankali kan muhimman bangarori 4 da suka shafi yaki da talauci_fororder_220215-faeza- poverty reduction

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun ya yi kira da a mayar da hankali kan muhimman bangarori 4 da suka shafi yaki da talauci da yunwa da suka hada da wadatar abinci da kare masu rauni da samun dorewar ci gaba da tabbatar da adalci tsakanin al’umma.

Zhang Jun ya yi wannan kira ne jiya, yayin taro na 60 na hukumar kula da ci gaban al’umma.

A cewarsa, annobar COVID-19 ta mayar da hannun agogo baya dangane da nasarar da duniya ta samu wajen rage fatara, lamarin da ya kara jefa mutane miliyan 140 cikin kangin talauci, inda kimanin mutane miliyan 800 ke fama da yunwa. Ya ce, annobar ta sa wasu kasashe masu tasowa sun kara komawa cikin talauci da rashin kwanciyar hankali, kana suna fuskantar kalubalen farfadowa bayan annobar. Yayin da a manyan kasashe kuma, rukunoni masu rauni na kara fadawa cikin wahalhalu, inda ake samun karuwar bukatar adalci a tsakanin al’umma.

Yayin da ci gaban duniya ke kan wata muhimmiyar gaba, Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar raya duniya ta shirin GDI yayin muhawara karo na 76 ta babban zauren MDD, wadda ta mayar da hankali kan muhimman bangarori 8 dake ingiza hadin kai da gudanar da shirye-shirye, domin aiwatar da matsayar da aka cimma da gaggauta aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta 2030 da kare muhalli da samun ci gaba bisa daidaito a duniya.

A watan Junairun da ya gabata, kasar Sin ta kaddamar da wani shiri na Rukunin Abokai Masu Rajin Samar da Ci Gaba a Duniya, a birnin New York, wanda ya samu karbuwa tsakanin kasashe mambobin MDD da hukumomi sama da 100. Sin na maraba da karin kasashe da hukumomi su shiga rukunin, ta yadda za a aiwatar da shirin a aikace da taimakawa kasashe, musamman masu tasowa da kawar da talauci da yunwa da cimma ci gaba na bai daya. (Fa’iza Mustapha)