logo

HAUSA

Shugaban IOC ya taya CMG murnar gabatar da shirye shirye masu kayatarwa yayin gasar Olympic ta birnin Beijing ta 2022

2022-02-15 20:08:10 CRI

Shugaban IOC ya taya CMG murnar gabatar da shirye shirye masu kayatarwa yayin gasar Olympic ta birnin Beijing ta 2022_fororder_CMG

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa IOC Mr. Thomas Bach, ya taya kafar CMG murnar watsa shirye shirye masu kayatarwa, yayin gasar Olympic ta birnin Beijing ta 2022 din nan.

Mr. Bach ya jinjinawa kwazon CMG, game da yayata shirye shirye masu gamsarwa, kamar dai yadda aka wallafa hakan, a shafin yanar gizo na kwamitin IOCn a Talatar nan.

Bugu da kari, yayin wata ganawa da shugaban CMG Shen Haixiong, Mr. Bach ya yi karin haske game da irin karbuwa da kafofin watsa shirye shiryen gasar suka samu. Ya ce ya zuwa ranar Juma’a 11 ga watan nan na Fabarairu, an kalli wannan gasa har tsawon sa’o’in talabijin biliyan 2.05 a cikin kasar Sin, adadin da ya haura na jimillar gasannin birnin PyeongChang na shekarar 2018, da na birnin Sochi na shekarar 2014 da kaso 15 bisa dari.

Domin martaba gudummawar da CMG ta bayar, da kuma dadadden hadin gwiwa tsakanin kafar da kwamitin IOC, Mr. Bach ya mikawa Mr. Shen kofin girmamawa na musamman. (Saminu)