logo

HAUSA

Wang Wenbin: Jirgin ruwan dakon kayan tallafi na Sin ya isa tsibirin Tonga

2022-02-15 20:37:12 CRI

Wang Wenbin: Jirgin ruwan dakon kayan tallafi na Sin ya isa tsibirin Tonga_fororder_汪文斌

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce da safiyar yau Talata, jirgin dakon kayan tallafi na Sin, mai dauke da sama da tan 1,400 na nau’o’in kayayyakin jin kai, ya isa tsibirin Tonga cikin nasara. Wang ya ce wannan ne karo na 4, da Sin ke gabatarwa tsibirin na Tonga kayan tallafi, bayan aukuwar bala’in aman wutar dutse, da ambaliyar ruwa mai karfin gaske da ta aukawa tsibirin.

A wani ci gaban kuma, Wang Wenbin ya ce Sin na fatan sashen tsare tsaren ayyuka, na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, zai gudanar da nazari mai zaman kan sa, game da burin kasar Japan na zubar da dagwalon nukiliyar Fukushima a ruwan teku, domin tabbatar da rashin hadarin hakan ga lafiyar al’umma.

A daya hannun kuma, jami’in ya ce kwace kadarorin kasar Afghanistan da Amurka ta yi, ba tare da amincewar al’ummar Afghanistan ba, tare da mayar da kadarorin mallakin Amurka tamkar fashi da makami ne. (Saminu)