logo

HAUSA

Firaministan Canada ya ayyana tunkarar batutuwan gaggawa domin kawo karshen zanga-zangar masu manyan motoci

2022-02-15 11:08:01 CRI

Firaministan Canada ya ayyana tunkarar batutuwan gaggawa domin kawo karshen zanga-zangar masu manyan motoci_fororder_220215-faeza- Canada

Firaministan Canada, Justin Trudeau, ya ayyana dokar tunkarar batutuwan gaggawa domin taimakawa lardunan kasar, shawo kawo karshen shingayen da aka kafa da jerin gwanon motoci sanadiyyar zanga-zanga.

Justin Trudeau, ya bayyana yayin wani taron manema labarai cewa, ya ayyana dokar ne karon farko a tarihin kasar, domin ba gwamnatin tarayya karin iko na wucin gadi, da nufin magance batutuwan dake akwai. Yana mai cewa, matakin zai shafi yankuna masu bukata ne kadai, ba dukkan kasar ba.

Dokar, wadda ta maye gurbin dokar yaki ta 1980, na samar da iko na musamman domin tunkarar yanayin gaggawa dake shafar walwalar jama’a kamar aukuwar iftila’i da barkewar cututtuka da rikice-rikice da matsalolin gaggawa a kasashen waje da kuma barkewar yaki. (Fa’iza Mustapha)