logo

HAUSA

Xi ya taya Steinmeier murnar sake zabarsa shugaban Jamus

2022-02-14 10:38:41 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya Frank-Walter Steinmeier murnar  sake zabarsa a mukamin shugaban tarayyar Jamus.

A sakon taya murnar da ya aika masa, Xi ya bayyana cewa, a wannan shekara ake bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Jamus.

Shugaba Xi yana dora muhimmanci kan ci gaban huldar dake tsakanin Sin da Jamus, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da Steinmeier domin bunkasa huldodin dake tsakanin kasashen Sin da Jamus daga dukkan fannoni. (Ahmad)