logo

HAUSA

Gine-ginen Olympics sun inganta tushen al’adun da suka shafi wasannin Olympics

2022-02-14 14:14:00 CRI

Gine-ginen Olympics sun inganta tushen al’adun da suka shafi wasannin Olympics_fororder_20220130_006_1397076

A sakamakon yadda kasar Sin ta samu damar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi, kasar ta aiwatar da jerin gine-ginen da suka shafi al’adun wasannin Olympics, wadanda suka fadada filayen wasannin ga al’umma, baya ga kara inganta tushen yayata al’adun wasannin Olympics na lokacin sanyi.

Bisa kididdigar da aka fitar, an ce, ya zuwa karshen shekarar bara, kasar Sin ta gina filaye 43, da suka shafi al’adun wasanin Olympics na lokacin sanyi, wadanda suka barbazu a sassa 19 na fadin kasar, inda aka ilmantar da al’umma kan al’adun wasannin Olympics na lokacin sanyi, da ma wasannin kankara, da al’adun gargajiya da dai sauransu, wadanda suka samar wa mazauna birnin damar fahimtar wasannin Olympics na lokacin sanyi, da ma shiga harkokin wasanni na lokacin sanyi.

Ban da haka, an kuma gina lambunan shakatawa na Olympics a sassa uku, da ake gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, inda ta hanyar yayata wasannin Olympics din aka fadada filayen wasanni ga al’umma, tare kuma da ingiza bunkasuwar wasanni, da al’adu, da ma harkokin yawon shakatawa a shiyyar baki daya.  (Lubabatu)