logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada aniyar tallafawa ayyukan gona

2022-02-14 10:16:54 CRI

Firaministan Sin ya jaddada aniyar tallafawa ayyukan gona_fororder_0214-Chinese premier-Ahmad

Firaiministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada aniyar tallafawa fannin aikin gona domin tabbatar da cigaban bunkasa samar da hatsi wanda ya zarta kilogram biliyan 650 cikin shekara guda.

Li ya yi wannan tsokaci ne a wani umarnin da ya bayar yayin taron kasa kan bunkasa ayyukan gona a lokacin bazara wanda aka gudanar a ranar Lahadi a lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.

A cewar firaministan, kamata ya yi a kara azama don tallafawa aikin gona, da bada tabbacin samar da kayan amfanin gona, da tabbatar da daidaita farashin kayan amfanin gonar, da kuma tabbatar da fara ayyukan noman bazara a kan lokaci.

Mataimakin firaministan Hu Chunhua ya halarci taron, kana ya gabatar da jawabi, inda ya bukaci a zage damtse wajen yin aiki tukuru domin cimma dukkan burikan ayyukan gona da ake son cimmawa a bana, da daidaita tsarin shuka hatsi, da fadada noman waken soya da amfanin gona da ake fidda mai, da kuma rage tasirin faruwar bala’u daga indallahi.  (Ahmad)