logo

HAUSA

MDD ta kammala matakin farko na tuntuba a Sudan don daidaita rikicin siyasar kasar

2022-02-14 11:12:10 CRI

MDD ta kammala matakin farko na tuntuba a Sudan don daidaita rikicin siyasar kasar_fororder_0214-Sudan-Ahmad

A jiya Lahadi shirin MDD a kasar Sudan ya kammala matakin farko na tuntubar bangarorin kasar Sudan da nufin kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar.

Sanarwar ta ce, shirin MDDr na tallafawa mika mulki a Sudan wato (UNITAMS), nan bada jimawa ba zai samar da wani takaitaccen kundi wanda zai bayyana muhimman bangarorin da aka cimma matsaya kansu a tsakanin masu ruwa da fagen siyasar kasar Sudan da kuma bangarorin da ake tababa kansu game da batun mika mulki ga farar hulda a kasar.

Volker Perthes, shugaban shirin na UNITAMS ya bayyana matakin tuntubar a matsayin muhimmin batu, kasancewar yana baiwa tawagar damar sauraron shawarwarin da al’ummun kasar Sudan ke gabatarwa.

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, a ranar Lahadi ya bukaci samun cikakken hadin kai daga bangarorin kasa da kasa da na shiyya domin cimma nasarar warware rikicin siyasar kasar.

Al-Burhan ya ce, burin gwamnatin kasar na warware rikicin ya kunshi kaddamar da cikakkiyar tattaunawa wacce za ta tattaro dukkan jam’iyyu da masu ruwa da tsaki cikin al’ummar kasar, in ban da haramtacciyar jam’iyyar National Congress Party, da kuma kafa gwamnati mai zaman kanta wacce ke da kwarewa domin ta jagoranci ragowar wa’adin da ya rage na mika mulki a kasar. (Ahmad)