logo

HAUSA

Shugaban Sudan ya ce sojoji sun bude kofar tattaunawar siyasar kasar

2022-02-13 15:45:30 CMG

Shugaban Sudan ya ce sojoji sun bude kofar tattaunawar siyasar kasar_fororder_0213-Sudan-Ahmad

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya jaddada cewa, kofar sojojin kasar a bude take domin shirya tattaunawa ta kasa da nufin cimma nasarar mika mulki ga gwamnatin demokaradiyya a kasar.

A yayin wata tattaunawar shugaban da aka watsa ta gidan talabijin na Sudan TV, Al-Burhan ya ce, sojojin kasar a shirye suke su gudanar da tattaunawa game da wa’adin mika mulki a kasar muddin aka cimma matsaya.

Ya ce, “Ko ni ko kuma hukumar sojojin kasar, babu wanda yake son dawwama a mulkin Sudan. Sojojin zasu sakarwa fagen siyasar kasar mara da zarar an yi nasarar gudanar da zabuka ko kuma an cimma maslaha a kasar."

Ya yi kiran a shiga tattaunawa wadda zata kunshi dukkan bangarorin kasar, in ban da jam’iyyar National Congress Party, ta tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

Bugu da kari, Al-Burhan ya soki lamarin tattaunawar da MDD ta shirya wanda Volker Perthes, shugaban tawagar tallafawa shirin mika mulki na MDD a Sudan (UNITAMS) ya jagoranta.

Yace, “Volker mai shiga tsakani ne wanda ya kamata ya tattaro dukkan bangarori domin a zauna a teburin tattaunawa, amma bashi da wani hurumin gabatar da wani tsari a kasar. Ya zauna da wasu tsirarun kungiyoyi kuma ya karkata kan shawarwari da tunaninsu.” (Ahmad)

Ahmad