logo

HAUSA

Gwamnatin Libya ta musanta murabus din ministocinta

2022-02-13 16:20:22 CMG

Gwamnatin Libya ta musanta murabus din ministocinta_fororder_0213-Libya-ahmad

Jiya Asabar, gwamnatin kasar Libya ta karyata rahotannin dake cewa  wasu daga cikin ministocin kasar sun yi murabus, inda ta tabbatar da cewa, gwamatin tana ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

A wata sanarwar da kakakin gwamnatin kasar, Mohammad Hamuda, ya fitar ya bayyana cewa, gwamnatin hadin kan kasar tana fuskantar jerin kalaman haifar da rudani da labaran bogi, wadanda suka kunshi wasu rubutattun bayanan karya da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani dake nuna cewa wasu ministocin kasar sun ajiye aikinsu.

Kakakin gwamnatin ya ce, “Dukkan ministocin kasar suna ci gaba da aikinsu kamar yadda aka saba kuma a halin yanzu ma suna ofisoshinsu.”

A kwanaki biyun da suka gabata, rahotanni sun karade kafafen sada zumunta na zamani game da batun yin murabus din wasu daga cikin ministocin gwamnatin Libya, da suka hada da ministar harkokin wajen kasar, Najla Mangoush.

A ranar Alhamis din da ta gabata majalisar wakilan jama’ar kasar Libyan ta kada kuri’ar amincewa da zaben Fathi Bashagha, tsohon ministan cikin gidan kasar, a matsayin sabon firaministan kasar Libya, inda ya maye gurbin Abdul-Hamid Dbeibah.(Ahmad)

Ahmad