logo

HAUSA

Juan Antonio Samaranch Jr.: Gasar Wasannin Olympics ta Lokacin Sanyi Ta Beijing Ta Zarce Tunanin IOC

2022-02-12 17:06:14 CRI

Bisa la’akari da yaduwar annobar COVID-19, ayyukan shirya gasar Olympics ta lokacin huturu ta Beijing, sun kasance masu matukar wahala, sai dai sun samu kyakkyawan yabo.

Shugaban kwamitin taimakawa shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta shekarar 2022 na kwamitin wasannin Olympic na duniya IOC, wato Juan Antonio Samaranch Jr. ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, duk da muhawarar da ake tafkawa kan kasashe masu karbar bakuncin gasanni da kwamitocin shirya gasannin, kwamitin IOC bai taba shakkun karfin kasar Sin na karbar bakuncin gasar ba, haka kuma ayyukan shirya gasar da aka yi, ba kawai cimma mizanin kwamitin IOC kadai suka yi ba, har ma da zarce tunaninsu.

A kokarin tabbatar da gudanar da gasar yadda ya kamata, ana gudanar da gasar tare da sa ido da takaita zirga-zirgar ‘yan wasa da jami’ai. A cewar Juan Antonio Samaranch Jr., hukumomin kula da lafiyar al’umma na kasar Sin sun yi aiki tukuru, inda wannan mataki da suka dauka, ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar wasannin ba tare da wata tangarda ba kawo yanzu.

Ya kara da cewa, gasar ta lokacin hunturu ta Beijing, za ta yi kyakkyawan tasirin kan zuriyoyi masu zuwa, kamar yadda gasar ta lokacin zafi ta shekarar 2008 ta yi.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin na da wuraren wasanni na gani na fada, wadanda za su cimma bukatun al’ummar kasar cikin shekaru da dama masu zuwa, yana mai cewa, ba kwanaki 16 kadai, sai an kai fiye da shekaru 60. Ya ci gaba da cewa, ababen more rayuwa kamar jiragen kasa masu sauri da manyan tituna, na da matukar muhimmanci ga al’umma, za su kara ingancin rayuwar jama’a. (Fa’iza Mustapha)