logo

HAUSA

Zhao Lijian: Taron sassa 4 wani yunkuri ne na dakile kasar Sin

2022-02-11 20:24:40 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce taron da manyan jami’an kasashen Amurka da Japan, da Australia da India suka shirya gudanarwa, wani salo ne na yunkurin dakile kasar Sin.

Zhao wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da ya gudana, ya ce sassan 4 na da burin amfani da taron na su, domin tattauna abun da suka kira “Karuwar tasirin Sin”.

Jami’in ya kara da cewa, wannan salo ne da Amurka ke bi domin wanzar da danniya, kuma hakan zai harzuka wasu sassa, tare da haifar da fito na fito, tare da gurgunta hadin gwiwar sassan kasa da kasa.

Zhao Lijian ya yi kira ga kasashen duniya, da su yi watsi da tsohon tsarin cacar baka, su gyara kura kuran su, game da kafa tawagogin da za su rika yiwa saura kallon hadarin kaji, ko raba kan kasashen duniya. Kaza lika ya bukaci sassan kasa da kasa, da su ba da gudummawa, wajen wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin Asiya da tekun fasifik.

A Juma’ar nan ne, sakataren wajen Amurka Antony Blinken, ya gana da ministocin harkokin wajen kasashen Japan, da Australia, da India a birnin Melbourne.   (Saminu)

Saminu