logo

HAUSA

Mutane hudu sun mutu a harin da ake zaton ’yan fashi sun kai a kudu maso yammacin Najeriya

2022-02-11 10:04:21 CRI

Mutane hudu sun mutu a harin da ake zaton ’yan fashi sun kai a kudu maso yammacin Najeriya_fororder_220211-attack in SW Nigeria-Ahmad1

Hukumar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane hudu, da suka hada da jami’an ’yan sanda biyu da kuma fararen hula biyu, inda wasu da ake zaton ’yan fashi da makami ne suka harbe su yayin wani harin da suka kai a jihar Oyo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya.

Lamarin dai ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a yankin Idi Ape dake Ibadan, babban birnin jihar, kamar yadda babbar jami’ar ’yan sandan yankin Ngozi Onadeko ta bayyana.

A cewarta har zuwa yanzu ba a kama kowa ba. Ta kara da cewa, alamu sun nuna cewa ’yan fashi da makamin sun buya a wani waje da ba tantance ba.

Ta ce an killace jihar domin hana ’yan fashin tserewa daga jihar.

Jami’ar ’yan sandan ta kara da cewa, jami’ansu da sauran hukumomin tsaron jihar sun yi hadin gwiwa domin damke ’yan fashin, sannan ta sanar cewa za a yiwa al’umma cikakken bayani kan lamarin a nan gaba. (Ahmad)