logo

HAUSA

CMG Ya Samar Da Kyamara Mai Saurin Daukar Hotunan Bidiyo Domin Gasar Wasannin Olympics Ta Beijing

2022-02-11 19:45:32 CRI

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya kera wata kyamara mai karkon gaske, bisa fasahar “Ultra HD 4K” domin amfani da ita wajen daukar hotunan bidiyo masu nagarta. Kyamarar dai na iya zarta gudun ‘yan wasan dake tsere a dandamalin kankara, yayin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing dake gudana yanzu haka.

An kafa kyamarar a cikin zauren tseren kankara na babban filin wasan hunturu dake birnin Beijing, inda kyamarar da aka yiwa lakabi da "Cheetah," kan yi gudun mitoci 25 ko wace dakika, wato kwatankwacin gudun kilomita 90 ko wace sa’a.

Bisa kiyasi, ‘yan wasan tseren kankara kan yi gudun mitoci 18 ne a duk dakika, kimanin kilomita sama da 60 zuwa 70 a duk sa’a, wanda hakan ke bukatar samar da na’ura da za ta iya bin su da saurin gaske, domin daukar motsi da suke yi, kamar karin sauri da raguwar sa, da wuce juna, da yadda suke sarrafa jikin su yayin da suke gudu.

Shugaban sashen samar da kayayyakin aiki na CMG Zhao Wei, ya jagoranci tawagar da ta gwada aiki da wannan kyamara, bayan shafe tsawon lokaci ana gudanar da bincike da tsara aikin ta. Tun da fari, an kafa kyamarar ne a wajen harabar dandalin da ake gudanar da tseren, kafin samun amincewar amfani da ita daga kamfanin dake jagorantar watsa shirye-shirye, na kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa IOC.   (Saminu)

Saminu