logo

HAUSA

Kasa da kasa sun kara nuna yabo ga gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing

2022-02-11 20:27:57 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin tana kokarin cika alkawarinta na gudanar da gasar wasannin Olympics mai tsaro da nagarta, kuma sassan kasa da kasa sun kara jinjinawa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing.

Zhao Lijian ya bayyana cewa, shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya, da shugaban babban taron MDD, da sarkin Cambodia, da shugaban Serbia, da yariman masarautar hadaddiyar daular Larabawa, da firaministan Pakistan, da sauran shugabannin kasa da kasa sun bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, za ta taimaka wajen shaida karfi da hadin gwiwa, da burin neman jin dadin zaman rayuwar bil Adama, kana ta shaida tunanin Olympics wato kara hada kai.

An gudanar da gasar bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19, wanda hakan ya shaida karfin kasar Sin na shirya gasar. (Zainab)