logo

HAUSA

Yan sanda na binciken barazanar harin bam a makarantu 6 na Washington, D.C.

2022-02-10 10:21:28 CRI

Yan sanda na binciken barazanar harin bam a makarantu 6 na Washington, D.C._fororder_0210-Ahmad1-bomb threats

Hukumar ’yan sandan Washington D.C. ta sanar cewa, ta fara gudanar da bincike game da barazanar harin bam a wasu makarantu shida dake yankunan babban birnin kasar Amurka.

Makarantun sun hada da, Dunbar High School, wacce a halin yanzu ake kokarin kwashe dalibanta, kamar yadda hukumar ’yan sandan babban birnin ta wallafa a shafin twita.

Matakin kwashewar na zuwa ne kwana guda bayan fitar da mutum na biyu Doug Emhoff daga wajen wani taro a makarantar Dunbar sakamakon barazanar harin bam.

Akwai makarantu da dama masu tarihin kwalejoji da jami’o’in bakaken fata da ake kira (HBCUs), a fadin kasar ta Amurka wadanda ke fuskantar barazanar harin bam a kwanakin farko na wannan wata wadanda aka ware su domin karrama gwagwarmayar da Amurkawa ’yan asalin kasashen Afrika suka yi a tarihin kasar Amurka.

Wani jami’in hukumar tsaro ya ce, hukumar leken asiri ta Amurka FBI ta gano wasu mutane shida wadanda ake zargin suna da hannu wajen haifar da bazaranar ga makarantun HBCUs. (Ahmad)