logo

HAUSA

Gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing ta sa kaimi kan sayayyar kayayyakin wasan kankara

2022-02-10 10:34:44 CRI

Gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing ya sa kaimi kan sayayyar kayayyakin wasan kankara_fororder_kankara

A kwanakin baya, wasu kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun gabatar da rahotanni cewa, gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin ta sa kaimi kan sayayyar kayayyakin wasan kankara na kasar Sin, har adadin kayayyakin da aka sayar da su ta yanar gizo ko a zahiri ya karu bisa babban mataki.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters na kasar Birtaniya ya gabatar da wani rahoto cewa, lokacin da aka kaddamar da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, adadin kayayyakin wasan kankara da aka sayar da su a dandalin kasuwancin yanar gizo na JD na kasar Sin ya karu har ninki biyu idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, kuma adadin kayayyakin wasan kankara da aka sayar da su a dandalin kasuwancin yanar gizo na Tmall ya karu da kaso 180 bisa dari, adadin kayayyakin wasan kankara mai laushi da aka sayar a dandalin shi ma ya karu da kaso 300 bisa dari.

Rahoton ya yi nuni da cewa, kamfanonin samar da kayayyakin wasan lokacin sanyi da kayayyakin wasan kankara na kasa da kasa su ma suna yin kokari domin sayar da kayayyakinsu a kasuwar kasar Sin, sakamakon tasirin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing dake gudana.(Jamila)