logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira a mai da hankali kan kalubalen ta’addancin ETIM

2022-02-10 13:16:41 CRI

CRI_fororder_驻联合国代表-张军

Jiya Laraba zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya yi kira ga kwamitin sulhun majalisar da kasashen duniya da su kara mai da hankali kan kalubalen ta’addanci na kungiyar ‘yan ta'adda ta gabashin Turkiyya ETIM, haka kuma su katse huldar dake tsakanin kungiyar da kungiyar IS.

Zhang Jun, ya fadi haka ne yayin taron da kwamitin sulhun ya kira domin tattauna batun kalubalen ta’addanci ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya jiya.

Yayin da yake tsokaci game da yadda ake taimakawa kasashen Afirka wajen kara karfafa yaki da ta’addanci, Zhang Jun ya bayyana cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana ba da goyon baya ga kasashen Afirka ta hanyoyi daban daban.(Jamila)