logo

HAUSA

Adadin mutanen da mahaukaciyar iskar Batsirai ta kashe a Madagaska ya kai 92

2022-02-10 10:30:05 CRI

Adadin mutanen da mahaukaciyar iskar Batsirai ta kashe a Madagaska ya kai 92_fororder_0210-Ahmad2-Madagascar

A kalla mutane 92 ne suka mutu sakamakon mahaukaciyar iska da ake kira Batsirai wadda ta faru a ranar 5 zuwa 6 ga watan Fabrairu a kasar Madagaska, kamar yadda rahoton baya bayan nan wanda ofishin hukumar yaki da annoba na kasar (BNGRC) ya wallafa a ranar Laraba.

Carole Ray, jami’ar hukumar BNGRC ta fada wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, a yankin Ikongo, galibin hasarar rayukan da aka samu sun faru ne sakamakon ruftawar gidaje da tumbatsar teku.

Ta ce, adadin mutuwar zai ci gaba da karuwar yayin da aka tattaro karin bayanai.

Alkaluman farko da aka samu sun nuna cewa, sama da mutane 110,000 iftila’in ya shafa, kana mutane 61,489 sun kauracewa muhallansu bayan da mahaukaciyar iskar ta tarwatsa yankunan kasar.

Bala’in iskar mai karfin gaske da ake kira Batsirai ta haifar da zaftarewar kasa a yammacin ranar Asabar a kasar Madagaska. (Ahmad Fagam)