logo

HAUSA

Mutane miliyan 13 na fama da yunwa a kahon Afrika

2022-02-09 09:41:15 CRI

Mutane miliyan 13 na fama da yunwa a kahon Afrika_fororder_220209-WFP-Faiza1

Shirin samar da abinci na duniya WFP, ya yi gargadin cewa, an yi kiyasin mutane miliyan 13 na fama da yunwa a kasashen Habasha da Kenya da Somalia, yayin da yankin kahon Afrika ke fama da matsanancin fari saboda rashin ruwan sama tun daga shekarar 1981.

Kakakin shirin WFP Tomson Phiri, ya shaidawa wani taron manema labarai a jiya cewa, akwai yuwuwa ta’azarar tasirin farin, inda dabbobi za su ci gaba da mutuwa tare da haifar da asara ga iyalai makiyaya.

Bayan shafe lokutan damina 3 a jere, ba tare da samun ruwan sama ba, girbin amfanin gona ya yi kasa da kaso 70 na yadda aka saba, a fadin yankunan da farin ya shafa.

A cewar WFP, zai kaddamar da wani shirin kai dauki ga yankin kahon Afrika, inda tuni tawagoginsa suka fara taimakawa iyalai da kudi da agajin gaggawa da samar musu da abinci da sinadaran gina jiki. (Fa’iza Mustapha)