logo

HAUSA

Sin tana da karfin bunkasa tattalin arziki mai inganci

2022-02-09 20:42:35 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, akwai shaidu dake nuna cewa, Sin tana da karfin bunkasa tattalin arziki mai inganci, mai ikon tabbatar da samar da kayayyaki ga duniya, kana ya sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, bisa yanayin tinkarar yaduwar cutar COVID-19, da farfado da tattalin arzikin duniya, Sin ta samu nasarori kan cinikin waje da jarin waje. Wannan ne kyakkyawan sakamakon da Sin ta samu, yayin da take kokarin kafa sabon tsarin samun bunkasuwa mai inganci, kana an shaida cewa, Sin tana son more damar samun bunkasuwa tare da sauran sassan duniya baki daya.

Bisa kididdigar da hukumomin Sin suka gabatar a kwanakin baya, yawan jarin waje da aka zuba a kasar Sin a shekarar 2021 ya karu sosai. Sin ta kasance kasuwa ta biyu mafi girma ta sayayyar kayayyaki a duniya, inda yawan kudin cinikin hajoji suka kai matsayin farko a tsawon shekaru 5 a jere, kana tana matsayi na biyu a jerin kasashen da suka fi jawo jarin waje a duniya. (Zainab)