logo

HAUSA

Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 ya zarce miliyan 400 a duniya

2022-02-09 10:37:35 CRI

Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar COVID-19 ya zarce miliyan 400 a duniya_fororder_src=http___imgs.tom.com_finance_202108_1026411992_CONTENT202108068e693d68f971ca99760x5000.jpg&refer=http___imgs.tom

Sabbin alkaluman da jami’ar John Hopkins ta Amurka ta fitar sun nuna cewa, zuwa karfe 5 da minti 21 na yammacin jiya Talata, agogon Amurka, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya zarce miliyan 400 a duk fadin duniya, yayin da ta yi sanadin mutuwar wasu 5,761,208.

Alkaluman sun shaida cewa, ya zuwa yanzu Amurka ta fi sauran kasashe samun yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar, da kuma yawan mace-mace. Sauran wasu kasashen da cutar ta fi yiwa muni sun hada da Indiya, da Brazil, da Faransa, da Birtaniya, da Rasha da kuma Turkiyya. (Murtala Zhang)