logo

HAUSA

Gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing za ta cimma burin kure fitar da iskar Carbon mai gurbata muhalli

2022-02-09 11:00:57 CRI

Gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing za ta cimma burin kure fitar da iskar Carbon mai gurbata muhalli_fororder_1

A matsayin gagarumar gasar wasannin motsa jiki ta kasa da kasa ta farko da aka shirya a kasar Sin, bayan da kasar ta tsara burikanta na kaiwa ga kololuwar iskar Carbon da take fitarwa, da kure fitar da iskar da kuma kawo karshenta, kiyaye muhalli ya zama wani batu mafi jan hankalin jama’a a yayin gasar ta bana. Ana amfani da makamashi maras gurbata muhalli a dukkan filaye gami da dakunan wasannin a bana, karo na farko ke nan, da ake amfani da wutar lantarki ba tare da gurbata muhalli ba dari bisa dari a filaye da dakunan wasannin a tarihin shirya gasar wasannin Olympics.

An samo yawancin wutar lantarkin da ake amfani da shi a yayin gasar ne daga wani yanki dake birnin Zhangjiakou na lardin Hebei, inda aka sauya albarkatun iska da haske a wurin, don su zama makamashin wutar lantarki ba tare da gurbata muhalli ba, abun da ya tabbatar da gudanar da gasanni yadda ya kamata a wasu manyan yankunan gasanni uku, da suka hada da Beijing, da Yanqing da kuma Zhangjiakou. (Murtala Zhang)