logo

HAUSA

Xi ya gana da wasu shugabannin kasashe da suka halarci bikin bude gasar Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing 2022

2022-02-07 10:47:31 CRI

Xi ya gana da wasu shugabannin kasashe da suka halarci bikin bude gasar Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing 2022_fororder_0207-Ahmad3-Xi Jinping

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Lahadi ya gana da wasu shugabannin kasashen duniya da suka halarci bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin sanyi ta Beijing 2022.

Yayin ganawarsa da sarki Grand Duke Henri na masarautar Luxembourg, shugaba Xi ya ce, kasar Sin tana matukar farin ciki bisa goyon bayan da Grand Duke Henri na masarautar Luxembourg yake baiwa kasar ta Sin tun daga lokacin gabatar da bukatar neman karbar bakunci da kuma shirye-shiryen gasar wasannin Olympic ta lokacin zafi a shekarar 2008 da kuma gasar wasannin motsa jiki ta lokacin sanyi ta shekarar 2022. Sannan ya godewa basaraken masarautar ta Luxembourg bisa goyon bayan da yake bayarwa da kuma yadda yake kokarin daga matsayin huldar dake tsakanin Sin da masarautar Luxembourg.

Haka zalika, a yayin ganawarsa da firaministan Mongoliya, Luvsannamsrai Oyun-Erdene, Xi ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da Mongolia domin zurfafa amincin dake tsakaninsu, da abokantaka gami da hadin gwiwa don karfafa huldar dake tsakanin Sin da Mongolia da nufin daga matsayin dangantakarsu zuwa sabon matsayi.

Bugu da kari, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Sadyr Zhaparov, shugaban kasar Kyrgyz, Xi ya ce, kasar Sin a shirye take ta zurfafa kyakkyawar huldar moriyar juna daga dukkan fannoni tare da kasar Kyrgyzstan, da nufin samar da karin alkhairai ga al’ummun kasashen biyu.

Shugaba Xi ya kuma ce kasar Sin a shirye take ta daga matsayin huldar dake tsakaninta da Kyrgyzstan a fannin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasashen biyu da kuma shiyyar. (Ahmad)