logo

HAUSA

Iran ta ce babu wasu bayanai da ta karba daga Amurka a tattaunawar Vienna

2022-02-07 10:07:27 CRI

Iran ta ce babu wasu bayanai da ta karba daga Amurka a tattaunawar  Vienna_fororder_0207-Ahmad1-Iran Nuke

Ministan harkokin wajen Iran ya ce, ya zuwa yanzu, kasar Iran ba ta karbi wasu bayanai daga kasar Amurka ba a yayin tattaunawar Vienna game da batun maido da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015.

Hossein Amir Abdollahian ya bayyana a yayin tattaunawa da gidan talabijin na IRIB mallaki gwamnati cewa, Iran ba ta samu wata gagaruma ko kuma muhimmiyar shawara daga kasar Amurka ba.

Ministan harkokin wajen na Iran ya ce, Tehran tana maraba da duk wani kudurin gwamnati ko kuma wani mataki daga gwamnatin Biden wanda zai taimaka wajen dage takunkuman da aka kakaba wa Iran bayan da Amurka ta dauki matakin kashin kanta na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar, wacce aka fi sani da JCPOA.

Da aka tambaye shi game da ko akwai yiwuwar cimma matsaya kan yarjejeniyar wucin gadi ta shekaru biyu, sai ya ce, “Muna neman kyakkyawar yarjejeniya ne, ba takaitacciya ba wacce za a saka mata wani wa’adi kayyadadde."

Gwamnatin Amurka ta sanar a ranar Juma’a cewa, tana janye takunkumai kan shirin nukiliyar fararen hular Iran, wanda zai bayar da damar hadin gwiwar kasa da kasa kan shirin nukiliyar kasar. (Ahmad)