logo

HAUSA

Kara hadin gwiwa da juna bisa tunanin Olympics ya dace da yanayin yanzu

2022-02-07 20:24:45 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kara hadin gwiwa da juna bisa tunanin Olympics, ya dace da yanayin yanzu.

A kwanakin baya, tsofaffin manyan shugabannin kasashen waje fiye da 10, da suka halarci dandalin tattaunawa na kasa da kasa na sada zumunta wato “Imperial Springs International Forum”, sun mika wasika ta hadin gwiwa ga shugaban kasar Sin, don nuna fatansu na gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing cikin nasara, inda suka yi kira ga gwamnatoci, da kungiyoyi, da al’ummun kasa da kasa, da su bi tunanin Olympics, wato “Hada kai domin kara saurin tafiya, da kara bunkasa, da kara karfi”, don warware matsaloli, tare da kirkiro makoma mai kyau ga dan Adam.

Zhao Lijian ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, ta samu goyon baya daga kasa da kasa. Kaza lika Sin tana son yin kokari tare da bangarori daban daban, don zurfafa hadin gwiwa a tsakanin jama’ar kasa da kasa, da kara imani, da karfi ga duniya dake fuskantar kalubalen yaduwar cutar COVID-19, don samar da kyakkyawar makoma tare. (Zainab)