logo

HAUSA

Jami’in Afrika CDC: Taron kolin AU zai haifar da sauyi kan yaki da annoba a Afrika

2022-02-07 10:16:14 CRI

Jami’in Afrika CDC: Taron kolin AU zai haifar da sauyi kan yaki da annoba a Afrika_fororder_0207-Ahmad2-AU summit

Darektan hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC, John Nkengasong, ya bayyana cewa, tsauraran matakan yaki da annobar COVID-19 da aka yi amfani da su a taron kolin shugabannin kungiyar tarayyar Afrika AU dake gudana, wanda shi ne karon farko da aka gudanar da taron gaba da gaba tun bayan barkewar annobar COVID-19, matakin zai kasance a matsayin hanyar tabbatar da sauye sauye a yaki da annobar.

Daga cikin tsauraran matakan kandagarkin cutar COVID-19 da aka dauka a wajen taron kolin, akwai gwajin cutar na wajibi da ake yiwa dukkan mahalartan kafin ba su damar halartar helkwatar kungiyar AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

A kwanaki ukun farko na taron, wanda ya kunshi taron tattaunawar shugabannin majalisar AU, hukumar dakile cutuka ta Afrika CDC ta yi nasarar gudanar da gwajin cutar sama da 5,400 ta hanyar amfani da cibiyoyin gwaje-gwaje na wucin gadi da aka kafa a harabar AU.

Daraktan ya ce, wannan taron kolin ya kasance mai kawo sauye-sauye game da yadda ake gudanar da manyan taruka da tattaunawar da ake shiryawa a nahiyar Afrika.

Ya zuwa yammacin ranar Asabar, an samu rahoton jimillar mutane 10,896,302 sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika. Kana yawan mutanen da annobar ta kashe a fadin nahiyar ya kai 241,112, yayin da masu fama da cutar 9,917,757 sun warke daga cutar. (Ahmad)