logo

HAUSA

Xi ya aika sakon taya murna ga Mattarella bayan ya sake samun damar jagorantar Italiya

2022-02-07 10:51:06 CRI

A ranar 4 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikawa takwaransa na kasar Italiya Sergio Mattarella, sakon murna bayan da ya sake samun damar jagorantar kasar, inda ya yi nuni da cewa, huldar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Italiya tana da tushe mai inganci, har ta bayar da abin koyi ga sauran kasashen duniya, yanzu haka kasashen biyu suna goyon bayan junansu wajen shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing na shekarar 2022 da na birnin Milan na shekarar 2026, ana iya cewa, sun samu sabbin damammakin ciyar da huldarsu gaba. Shugaba Xi ya kara da cewa, yana son yin kokari tare da shugaba Sergio Mattarella domin zurfafa amincin siyasa dake tsakanin kasashen biyu, tare kuma da kara habaka cudanya da hadin gwiwa a fannoni daban daban, ta yadda kasashen biyu da al’ummunsu za su ci gajiya. (Jamila)