logo

HAUSA

Xi ya aikewa sarauniya Elizabeth II sakon murna

2022-02-07 14:01:51 CRI

Jiya ranar 6 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa sarauniya Elizabeth II sako domin taya ta murnar cika shekaru 70 da hawa kujerar sarautar Ingila, inda ya yi nuni da cewa, cikin dogon lokaci sarauniya Elizabeth II tana mai da hankali matuka kan zumuncin dake tsakanin kasarta da kasar Sin, kuma tana kokarin ciyar da huldar dake tsakanin kasashen biyu gaba.

Xi ya kara da cewa, bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Birtaniya, yana fatan kasashen biyu za su yi amfani da wannan damar domin kara zurfafa amincin dake tsakaninsu, tare kuma da kara habaka cudanya da hadin gwiwa dake tsakaninsu. (Jamila)