logo

HAUSA

Senegal ta lashe kofin kwallon kafan Afrika a karon farko

2022-02-07 14:57:51 CRI

Senegal ta lashe kofin kwallon kafan Afrika a karon farko_fororder_0207-Ahmad5-AFCON

Kasar Senegal ta yi nasarar karbe kambun kofin kwallon kafan Afrika bayan da kungiyar wasan Teranga Lions ta kasar ta yi nasarar lashe kofin gasar AFCON, inda ta lallasa Masar a wasan karshe a bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka gudanar da yammacin ranar Lahadi.

Bayan fafatawa mai zafi da suka gudanar, dan wasan Senegal mafi daraja kana dan wasan gaban kasar Mane, yayi nasarar zura kwallon da ta baiwa Senegal damar lashe gasar da ci 4 da 2 tsakaninta da Masar, inda kasar ta samu nasarar lashe kofin na AFCON a karo na farko.

Bayan rashin nasarar da kasar ta samu yayin da ta kai matakin karshe a gasar AFCON a shekarun 2002 da 2019, a yanzu, Senegal ta farfado da martabarta a fagen gasar kwallon kafan Afrika yayin da lashe gasar wacce aka buga a filin wasan Olembe dake Yaounde, babban birnin kasar Kamaru. (Ahmad)