logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Monaco sun yi hira kan Bingdundun yayin ganawarsu

2022-02-07 10:48:24 CRI

Shugabannin Sin da Monaco sun yi hira kan Bingdundun yayin ganawarsu_fororder_xi

Jiya ranar 6 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ganawa da takwaransa na kasar Monaco, Albert Alexandre Louis Pierre Grimaldi, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar, inda suka yi musanyar ra’ayoyi mai zurfi kan yadda za su kara ciyar da huldar dake tsakanin kasashensu gaba, kuma sun yi hira kan kayan alamar musamman na wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing wato Bingdundun.

Kwanan baya, shugaban Monaco ya taba yin gwajin samar da kayan Bingdundun da garin alkama yayin halartar liyafar da aka shirya a babban dakin taron jama’a domin maraba da zuwansu kasar Sin, inda ya gabatar da rokonsa cewa:

“Ko zan iya gabatar da rokona? Ina son samar da wani Bingdundun na daban, saboda ina da tagwaye guda biyu, ina bukatar Bingdundun guda biyu, domin baiwa yara kyauta bayan na dawo gida.”

Yayin ganawarsu jiya, shugaba Xi shi ma ya bayyana cewa,

“Na ji an ce, kana son baiwa yaranka tagwaye Bingdundun bayan dawowarka gida, shi ya sa kana bukatar guda biyu, sai ka zabi Bingdundun guda biyu, ka baiwa yaranka tare da fatan alheri, ina fatan za su nuna sha’awa kan wasan kankara kamar yadda kake nunawa, har su kasance fitattun ‘yan wasan kankara.”

A baya shugaban kasar Monaco Albert Alexandre Louis Pierre Grimaldi ‘dan wasan sana’a ne na lokacin sanyi, shi ma ya taba shiga gasar keken kankara mai laushi na wasannin Olympics na lokacin sanyi inda ya wakilci kasarsa ta Monaco har sau biyar.(Jamila)