logo

HAUSA

Babban jami’in MDD ya bukaci a fadada zuba jari a Afrika

2022-02-06 17:34:38 CMG

Babban jami’in MDD ya bukaci a fadada zuba jari a Afrika_fororder_0206-UN-AU-Ahmad

Sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, yayi kiran a kara fadada zuba jari a nahiyar Afrika.

Babban sakataren, yayi wannan tsokaci ne a yayin gabatar da jawabi a taron kolin shugabannin kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 35 wanda ya halarta ta kafar bidiyo, kuma wannan ne karon farko da shugabannin na Afrika suka gana gaba da gaba tun bayan barkewar annobar COVID-19.

Guterres ya fadawa shugabannin Afrika cewa, cimma nasarar muradun samar da dawwamamman cigaba ya dogara ne kan taimakawa zuba jari mai yawan gaske don karfafa tsarin kiwon lafiya da ilmi, da fannin samar da ayyukan yi, musamman a fannonin makamashi mai tsafta, da samar da tsarin kariya ga al’umma na bai daya, da tabbatar da daidaiton jinsi, da kuma samar da damammaki ga matasan Afrika.

Taron kolin na wuni biyu na AU, yana gudana ne tsakanin 5 zuwa 6 ga watan Fabrairu, a helkwatar kungiyar tarayyar Afrika AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, taken taron na bana shine, “Gina muhimmin sauyi a fannin abinci mai gina jiki a nahiyar Afrika: Gaggauta samar da cigaban dan adam, da cigaban zamantakewa, da bunkasar tattalin arziki."(Ahmad)

Ahmad