logo

HAUSA

Iran ta ce tana duba yuwuwar samun moriyar tattalin arziki a tattaunawar batun nukiliyarta

2022-02-06 17:28:57 CMG

Iran ta ce tana duba yuwuwar samun moriyar tattalin arziki a tattaunawar batun nukiliyarta_fororder_0206-Iran-Faeza

Sakataren majalisar koli ta tsaron Iran, Ali Shamkhani, ya yi kira ga Amurka, ta janye takunkumanta domin kasarsa ta samu moriyar tattalin arziki.

Ali Shamkhani, ya wallafa jiya a shafin tweeter cewa, samun moriyar tattalin arziki na hakika, muhimmin sharadi ne ga kulla yarjejeniya a tattaunawar Vienna dake gudana. 

Da yake mayar da martani game da batun dage taukunkumin da Amurka ta yi ranar Juma’a, wanda zai ba da damar hadin gwiwa kan ayyukuan nukiliya tsakanin Iran da kasashen duniya, jami’in ya ce wannan ba abu ne da za a iya amfana da shi ba. 

Da farko a ranar Juma’ar, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh, shi ma ya ce dage takunkumin da Amurka ta yi domin farfado da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 kawai, bai wadatar ba.

An cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran ne a shekarar 2015. Sai dai, a watan Mayun 2018, tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya janye kasar daga yarjejeniyar, inda ya kakabawa Iran takunkumai, wadanda daga baya suka kai Iran din ga saba alkawurranta, har ta sake fadada shirye-shiryenta na nukiliya da a baya ta dakatar. (Fa’iza Mustapha)

Faeza