logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da wasu manyan kusoshin kasa da kasa

2022-02-06 16:41:30 CRI

Wang Yi ya gana da wasu manyan kusoshin kasa da kasa_fororder_752

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da babban magatakardan MDD Antonio Guterres, a jiya Asabar.

A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan babban magatakardan da ma MDD baki daya, domin ba da gudummawa wajen aiwatar da harkokin majalisar. Kana kasar Sin tana fatan hada gwiwa da MDD domin raya huldar kasa da kasa, da kuma aiwatar da shawarar raya kasashen duniya.

A nasa bangare kuma, malam Guterres ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar sauye-sauyen yanayi cikin kasashen duniya, shi ya sa, karfafa taken Olympics na hadin gwiwa da taikamawa juna a wannan muhimmin lokaci, yake da muhimmanci. Ya ce shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar raya kasa da kasa a lokacin da ya dace, kuma MDD tana son goyon bayan kasar Sin da hada gwiwa da ita, wajen inganta wannan shawara.

Haka kuma, Wang Yi ya gana da babban sakataren kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da ministar harkokin wajen kasar Mongolia. (Maryam)