logo

HAUSA

Xi: Sin ba ta son tashin hankali, haka kuma bata tsoro

2022-02-06 16:27:33 CRI

Da safiyar yau Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Pakistan Imran Khan, wanda ya halarci bikin bude gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. A yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare yanayin adalci cikin harkokin kasashen duniya, kuma kasar Sin ba ta son tashin hankali, amma kuma, ba ta tsoronsa. Ya ce, kasar Sin tana da imani da karfin kare ’yancinta, da tsaro, da kuma ikonta na neman ci gaba.

Xi ya jaddada cewa, yanzu, an shiga yanayin sauye-sauye a duniya, shi ya sa, dangantakar diflomasiyya bisa manyan tsare-tsare da aka kulla tsakanin kasar Sin da kasar Pakistan take da muhimmiyar ma’ana. Ya ce ya kamata kasashen biyu su karfafa fahimtar juna da hadin gwiwa, domin habaka harkokin hadin gwiwa a tsakaninsu.

A nasa bangare kuma, firaminista Imran Khan na kasar Pakistan ya ce, a halin yanzu, ba wanda zai iya hana ci gaban kasar Sin, kana kasarsa da kasar Sin aminai ne. Ya ce kasar Pakistan tana tsayawa tsayin daka wajen hada kanta da kasar Sin a ko da yaushe.

Har ila yau, a yau din, Xi Jinping ya gana da takwararsa na kasar Singapore Halimah Yacob, da shugaban kasar Poland Andrzej Duda, da shugaban kasar Argentina Alberto Fernandez, da wasu manyan jami’an kasashen duniya. (Maryam)