logo

HAUSA

Mutane shida sun jikkata a fashewar bam a arewacin Kongo DRC

2022-02-06 17:33:20 CMG

Mutane shida sun jikkata a fashewar bam a arewacin Kongo DRC_fororder_0206-Congo-Ahmad

A kalla mutane shida ne suka samu raunuka a sakamakon fashewar bam da aka hada a cikin gida a wata kasuwa dake birnin Beni, a shiyyar arewa maso gabashin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, kamar yadda wata majiya ta shedwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Daga cikin wadanda lamarin ya shafa akwai mata da kananan yara, a cewar kafar yada labarai ta cikin gidan kasar, sannan wani mutum guda ya samu rauni mai tsanani inda aka garzaya dashi zuwa babban asibitin Beni don ba shi kulawa.

A yanzu haka dai jami’an tsaro tare da wasu jami’ai masu tantance boma-bomai da aka tura wajen sun killace inda bam din ya fashe domin tantance yanayin da ake ciki da kuma takaita hasarar da aka samu a kasuwar.

Hukumomin jami’an tsaro a yankin sun bukaci mazauna yankin da su sanya ido, kana hukumomin zasu sanar da cikakken bayani game da lamarin a nan gaba.

A kalla mutane takwas ne aka kashe a harin kunar bakin wake na baya bayan nan da ya faru a birnin Beni a ranar 25 ga watan Disamba, a lokacin da ake tsaka da gudanar da bikin kirsimeti.(Ahmad)

Ahmad