logo

HAUSA

Xi Jinping: Sin za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan MDD

2022-02-05 21:16:29 CRI

Xi Jinping: Sin za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan MDD_fororder_src=http___n1.itc.cn_img8_wb_sohulife_2021_06_19_162406500265797545.JPEG&refer=http___n1.itc

Yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya zo kasar Sin don halartar bikin budewar gasar Olympic ta lokacin sanyi ta 2022.

Xi Jinping ya nuna cewa, akwai manyan ayyuka 3 da za a mai da hankali a yau da kuma nan gaba yayin da ake kula da harkokin kasa da kasa. Na farko, hadin kai don yakar COVID-19. Na biyu ingiza samun bunkasuwa. Na uku yayata demokuradiyya. Kuma a nata bangare Sin za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan MDD da taka rawa wajen kiyaye zaman lafiya da bunkasuwa da kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya.

A nasa jawabin António Guterres ya nuna cewa, yadda kasar Sin ta samarwa duniya da alluran rigakafi biliyan 2, yana taimakawa aikin yakar COVID-19. Ya ce, shawarar da Xi Jinping ya gabatar ta raya duniya baki daya na da babbar ma’ana wajen ingiza ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekara 2030 da MDD ta gabatar, da warware matsalar rashin samun daidaiton bunkasuwa tsakanin kasashe daban-daban. Ya kara da cewa, MDD na fatan ganin Sin ta kara hada kai da MDD, kuma yana mai fatan ta taka muhimmiyar rawa wajen kyautata tsarin duniya da daidaita sauran matsaloli. (Amina Xu)