logo

HAUSA

Jami’in AfCFTA: Afrika tana maraba da taimakon kasar Sin na bunkasa fitar da kayayyaki ketare

2022-02-05 20:34:25 CMG

Jami’in AfCFTA: Afrika tana maraba da taimakon kasar Sin na bunkasa fitar da kayayyaki ketare_fororder_0205-AFCFTA-Ahmad

Babban jami’in kungiyar kasuwanci ta Afrika yayi maraba da muhimmin taimakon da kasar Sin ta gabatarwa kungiyar tarayyar Afrika AU wajen taimaka mata don bunkasa fitar da hajoji zuwa ketare nan da wasu shekaru masu zuwa.

Wamkele Mene, babban sakataren yarjejeniyar kasuwanci marar shinge ta kasashen Afrika (AfCFTA), ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Afrika tana maraba da zuba jarin kasar Sin da kuma hadin gwiwar kasuwanci don amfanawa juna a tsakanin bangarorin.

Mene yace, sun yabawa muhimmin kudirin da kasar Sin ta gabatar don bunkasa harkokin fitar da kayayyakin Afrika zuwa ketare. Sannan daidaikun kasashen Afrika, da ma shiyyoyinta, suna kara samun ingantuwa a kullum, jami’in ya bayyana hakan ne a gefen taron kolin shugabannin AU karo na 35(Ahmad)

Ahmad