logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashe daban-daban

2022-02-05 16:34:24 CRI

Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashe daban-daban_fororder_bd3eb13533fa828ba7ec3d11be04963d960a5a1d

Yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabannin kasashe daban-daban da suka halarci bikin bude gasar Olympic ta lokacin sanyi da aka gudanar a birnin Beijing a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.

Yayin ganawarsa da takwaransa na Masar Abdel Fattah al Sisi, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin Sin da Masar, ta zama abin koyi ga hadin kai da samun moriya tare tsakanin Sin da kasashen Larabawa da Afrika da ma kasashe masu tasowa. Ya ce, ya kamata bangaroin biyu su kara hada kai don ingzia burin tabbatar da kyakkyawar makomar kasashen biyu ta bai daya.

A nasa bangare, Shugaba Abdel Fattah al Sisi ya ce, bikin bude gasar Olympics ya yi kyau matuka, abin da ya bayyana karfin da Sin take da shi. Ya ce, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta ingiza bunkasuwar tattalin arzikin Masar, kuma kasar na fatan ci gaba da taka rawa a cikin shawarar.

Haka kuma, shugaba Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar  Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev da na kasar Turkmenistan Gurbanguly Berdymuhamedov da na kasar Serbia Aleksandar Vučić da babban sakataren MDD António Guterres sauransu. (Amina Xu)