logo

HAUSA

Sin da Rasha sun sake jaddada goyon bayansu kan muhimman muradunsu da nuna adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashensu

2022-02-05 17:05:46 CMG

Sin da Rasha sun sake jaddada goyon bayansu kan muhimman muradunsu da nuna adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashensu_fororder_0205-Rasha-Sin-Ibrahim

Kasashen Sin da Rasha, sun jaddada goyon bayansu ga muhimman muradunsu, da ‘yancin mallakar kasa, da cikakken ikon yankunansu, tare da nuna adawa da tsoma bakin kasashen waje a harkokinsu na cikin gida. Hakan na kunshe cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar jiya Juma'a, bayan wata ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu.

Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin na ziyara a kasar Sin. Kuma shugabannin kasashen biyu sun yi shawarwari a nan birnin Beijing, daga bisa ni kuma, sun halarci bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ta shekarar 2022 karo na 24.

Sanarwar ta ce, kasashen biyu, na adawa da kara fadada kungiyar tsaro ta NATO, don haka, sun bukaci kungiyar ta NATO, da ta yi watsi da tunaninta na yakin cacar baka, ta mutunta 'yancin kai,da tsaro da muradun sauran kasashe, ta kuma rike gaskiya da rikon amana ga ci gaban zaman lafiya a sauran kasashe.

Kasashen Sin da Rasha sun tsaya tsayin daka, kan duk wani yunkuri na kafa wata kungiya ta musamman da daidaita hulda a tsakanin kasashen yankin Asiya da tekun fasifik. Haka kuma suna yin taka-tsan-tsan game da mummunan tasirin dabarun Amurka game da shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tekun Indiya da fasifik.

Sanarwar ta kara da cewa, bangarorin biyu sun kuduri aniyar gina tsarin tsaro mai cike da daidaito, da bude kofa ga kasashen Asiya da tekun Pasifik, wanda ba ya nufin yakar kowace kasa ta uku, kuma suna kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata.(Ibrahim)

Ibrahim