logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya yi kira da a samar da hadin kai yayin da ake fama da annobar COVID-19

2022-02-05 20:55:05 CMG

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a samu hadin kai, da kara fahimtar juna a tsakanin kasashen duniya, domin dakile annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya.

Li ya bayyana haka ne, a lokacin da yake ganawa da babban daraktan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus da ke ziyara a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A jawabinsa Tedros ya ce, hukumar WHO tana matukar yabawa kokarin gwamnati da jama'ar kasar Sin wajen yakar cutar.

Ibrahim